Kasar Iran Ta Jinjinawa Afirka Ta Kudu Kan Karar Yahudawan Sahayoniyya Da Ta Yi A Kotun ICC

Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta yaba da matakan shari’a da kasar Afirka ta Kudu ta dauka kan gwamnatin yahudawan sahayoniyya Babban mai shigar da kara

Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta yaba da matakan shari’a da kasar Afirka ta Kudu ta dauka kan gwamnatin yahudawan sahayoniyya

Babban mai shigar da kara na Jamhuriyar Musulunci ta Iran, Sheikh Mohammad Mowahedi Azad, ya yaba da matakan shari’a da hukumomin shari’a na kasar Afirka ta Kudu suka dauka kan yahudawan sahayoniyya a matakin kasa da kasa, yana mai bayyana goyon bayan Iran ga wadannan matakai.

A wata ganawar da ta gudana tsakanin manyan masu shigar da kara na kasashen biyu a jiya Laraba, a gefen zaman taron masu gabatar da kara na kasashen kungiyar BRICS karo na shida, wanda aka gudanar a birnin St. Petersburg na kasar Rasha, Movahedi Azad ya ce: Wannan jaruntaka ce. daukar matakan kare al’ummar Falastinu da ake zalunta kuma lamarine da ya karfafa matsayin Afirka ta Kudu a matakin kasa da kasa sannan matsayi ne mai muhimmanci kuma ya kasance abin sha’awa ga al’ummomin duniya.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments