Jayayya Tsakanin Jakadun Kasashen Hadaddiyar Daular Larabawa Da Sudan A Kwamitin Sulhu

An yi jayayya tsakanin jakadun kasashen Hadaddiyar Daular Larabawa da Sudan a kwamitin sulhun Majalisar Dinkin Duniya Rikici ya barke tsakanin jakadun kasashen Sudan da

An yi jayayya tsakanin jakadun kasashen Hadaddiyar Daular Larabawa da Sudan a kwamitin sulhun Majalisar Dinkin Duniya

Rikici ya barke tsakanin jakadun kasashen Sudan da Hadaddiyar Daular Larabawa a kwamitin sulhun Majalisar Dinkin Duniya kan zargin da gwamnatin Sudan ta yi na cewa; Hadaddiyar Daular Larabawa tana bayar da makamai da goyon baya ga ‘yan tawayen Sudan na dakarun kai daukin gaggawa a rikicin da ake yi a Sudan da ya shafe tsawon watanni 14 ana gwabzawa.

Jakadan Hadaddiyar Daular Larabawa a Majalisar Dinkin Duniya, Mohammed Abu Shehab, ya ce jakadan Sudan a Majalisar Dinkin Duniya, Al-Harith Idris Al-Harith, ya yi zargi maras tushe kuma na  karya don kawar da hankalin duniya kan manyan laifukan da ke faruwa a kasarsa.

Yaki dai ya barke ne a kasar Sudan tun a tsakiyan watan Afrilun bara tsakanin sojojin Sudan da dakarun kai daukin gaggawa na Rapid Support Forces, sakamakon takaddama kan shirin mika mulki ga farar hula.

Majalisar Dinkin Duniya ta ce kimanin mutane miliyan 25, ko kuma rabin al’ummar Sudan, na bukatar agajin jin kai, a daidai lokacin da matsalar yunwa ke kara kamari a kasar, kuma mutane kusan miliyan takwas ne suka tsere daga muhallinsu.

Jakadan Sudan ya ce a gaban kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya: Hare-haren soji da dakarun kai daukin gaggawa na Rapid Support Forces sun fi shafar fararen hula, kuma kasar Hadaddiyar Daular Larabawa ce take aikewa da makaman ga ‘yan tawayen.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments