Iran : Jagora Ya Yi Fursunoni 2,654 Afuwa Alfarmar Bikin Babbar Sallah

Jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran, Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya amince da yin afuwa ko sassauta hukunce-hukuncen da aka yankewa wasu fursunoni 2,654

Jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran, Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya amince da yin afuwa ko sassauta hukunce-hukuncen da aka yankewa wasu fursunoni 2,654 a daidai lokacin da ake gudanar da bukukuwan babbar Sallah da kuma Eid al-Ghadir.

Bisa bukatar alkalin alkalai na kasar Gholmhossein Mohseni-Ejei, Ayatullah Khamenei ya amince da yin afuwa ko ko saukake hukunce-hukuncen da aka yanke mutanen.

Daga cikin wadanda aka yi wa afuwar, 182 mata ne, 30 kuma ‘yan kasashen waje ne, 53 kuma wadanda aka yankewa hukunci ne saboda dalilai na tsaro, 6 kuma ‘yan kasa da shekara 18 ne.

Dama Jagora ya saba a irin wannan lokaci na manyan bukukuwa yin afuwa ko sassauta hukunci ga fursunoni a fadin kasar.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments