Kasar Iran Ta Jaddada Wajabcin Karfafa Hadin Gwiwar Tattalin Arziki Tsakanin Kasashen Yankin

Mukaddashin ministan harkokin wajen Iran ya bayyana cewa: Karfafa haɗin gwiwar tattalin arziki ya zama dole don samun kwanciyar hankali a yankin Gabas ta Tsakiya

Mukaddashin ministan harkokin wajen Iran ya bayyana cewa: Karfafa haɗin gwiwar tattalin arziki ya zama dole don samun kwanciyar hankali a yankin Gabas ta Tsakiya

Mukaddashin ministan harkokin wajen kasar Iran Ali Baqiri Kani ya bayyana cewa: Iran da abokanta na kasar Iraki da dukkan kasashen yankin suna tabbatar da cewa zaman lafiya da wanzar da tsaron yankin ya dogara ne kan hadin gwiwa tsakanin bangarorin yankin, kuma Iran tana ganin ci gaban hadin gwiwar tattalin arziki ya zama wajibi domin samun kwanciyar hankali a yankin.

A jiya Juma’a ne Ali Baqiri ya bayyana hakan, a wani taron manema labarai na hadin gwiwa tare da fira ministan yankin Kurdawan Iraki Masrour Barzani inda ya ce: Yana mika godiyarsa ga al’ummar Iraki da yankin Kurdawan kasar bisa goyon baya da nuna juyayi ga shahadar jami’an Iran wato Shugaban kasa da Ministan Harkokin Waje da mukarrabansu.

Ya kara da cewa: Abokan da suke yankin Kurdawan kasar Iraki sun kasance tare da Iran da gaske a cikin wannan bala’i, ko ta hanyar aikewa da sako da kuma kasancewarsu a cikin wakilan siyasar Iran a kasashen waje, ko kuma kasancewarsu a birnin Tehran, kuma sun taka rawar gani sosai wajen kwantar da hankula da sassauta radadin gwamnati da al’ummar Iran cikin wannan babban bala’i.

Baqiri ya ci gaba da cewa: Dangantakar Iran da ‘yan uwansu na yankin Kurdawan Iraki ‘yan uwantaka ce ta kud da kud, kuma ta samo asali ne tsawon tarihi, a fagen al’adu, da kuma makoma ta bai daya a nan gaba, kuma bangarorin biyu sun haifar da wata alaka da ba za ta gushe ba a tsakaninsu.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments