‘Yan Majalisar Dokokin Kasar Afirka Ta Kudu Sun Zabi Cyril Ramaphosa A Matsayin Sabon Shugaban Kasa

Yan Majalisun Dokokin Kasar Afirka ta Kudu sun kada kuri’ar zaben Cyril Ramaphosa a matsayin sabon shugaban kasar Afirka ta Kudu a karo na biyu

Yan Majalisun Dokokin Kasar Afirka ta Kudu sun kada kuri’ar zaben Cyril Ramaphosa a matsayin sabon shugaban kasar Afirka ta Kudu a karo na biyu

A yammacin jiya Juma’a ne ‘yan Majalisar Dokokin Kasar Afirka ta Kudu suka zabi Cyril Ramaphosa dan shekaru 71 a duniya a matsayin sabon shugaban kasar a karo na biyu da kuri’u 283 na majalisar dokokin kasar da ta fito daga zaben ‘yan majalisar dokokin kasar da aka gudanar kwanan nan, wanda ya kunshi wakilai 400.

Mai shari’a Raymond Zondo, wanda ya jagoranci zaman zaben, ya ce, “An ayyana mai girma Cyril Ramaphosa a matsayin zababben shugaban kasa,” bayan da ya samu nasara a kan dan takarar jam’iyyar Economic Freedom Fighters mai ra’ayin rikau, Julius Malema, wanda ya samu kuri’u 44 na ‘yan Majalisar.

A daya hannun kuma, jam’iyyar African National Congress mai Mulki da babbar abokiyar hamayyarta, na masu goyon bayan ‘yan kasuwa karkashin jagorancin farar fata ta Democratic Alliance, sun amince da yin aiki tare a sabuwar gwamnatin hadin kan kasa, a wani sauyi da ya zo bayan shekaru 30 na mulkin jam’iyyar African National Congress.

Ba a taba tunanin wata rana za a cimma yarjejeniya tsakanin bangarorin biyu masu adawa da juna ba, kuma wannan yarjejeniya tana wakiltar sauyin siyasa mafi muhimmanci a kasar tun bayan da Nelson Mandela ya jagoranci jam’iyyar Congress Party har ta samu nasara a zaben shekara ta 1994 da ya kawo karshen mulkin wariyar launin fata a kasar.

A bangare guda kuma, Jam’iyyar Congress Party ta rasa rinjayenta a karon farko a zaben da aka gudanar a ranar 29 ga watan Mayu, kuma ta shafe makonni biyu tana tattaunawa da wasu jam’iyyun da aka kammala a safiyar Juma’a tare da kiran zaman sabuwar majalisar kasar.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments