Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran Nasir Kan’ani ya yi Allah wadai da kisan gilla da kuma raunata daruruwan mutanen da ba su ji ba ba su gani ba a kauyen Wad Al-Nura na kasar Sudan.
Nasir Kan’ani ya bayyana kisan gillar da kuma raunata daruruwan mutanen da ba su ji ba ba su gani ba, da suka hada da mata da kananan yara, a harin da aka kai kauyen Wad Al Noura a matsayin wani lamari mai ban tsoro.
Ya kara da cewa: Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta damu da ci gaba da yakin basasa a kasar Sudan da kuma mummunan halin da ‘yan kasar da ba su ji ba ba su gani ba suke ciki a yankuna daban-daban na wannan kasa.
Ya kuma jajantawa iyalan wadanda rikicin ya rutsa da su, ya kuma bukaci a dawo da zaman lafiya da matakan aminci a wannan kasa da kuma gaggauta dakatar da kashe-kashe na kisan kiyashi da ake yi a kasar Sudan.
Ya jaddada alhakin da ya rataya a wuyan kasashen duniya musamman hukumomin kare hakkin bil adama na su dauki kwararan matakai don kawo karshen halin da ake ciki a Sudan.