Iran Ta Jadadda Wajabcin Sassauta Rikice-rikice A Yankin

Iran ta bakin ministan harkokin wajen kasar na rikon kwarya Ali Bagheri Kani ta jaddada wajabcin sassauta rikici da warware rikice-rikice a yammacin Asiya. Mista

Iran ta bakin ministan harkokin wajen kasar na rikon kwarya Ali Bagheri Kani ta jaddada wajabcin sassauta rikici da warware rikice-rikice a yammacin Asiya.

Mista Kani, ya bayyana hakan ne yayin wani taron manema labarai na hadin guiwa da takwaransa na Iraki Fuad Hussein a birnin Bagadaza ranar Alhamis.

 Yana mai cewa ‘’kasashen biyu masu makwabtaka da juna Iran da Iraki su ne manyan ginshikai na tsaro a yankin mai matukar muhimmanci.

Babban jami’in diflomasiyyar na Iran ya bayyana abin da ke faruwa a zirin Gaza a matsayin laifin yaki tare da jaddada cewa dole ne a dakatar da kisan kiyashin da Isra’ila ke yi a yankin Falasdinu.

“Ya kamata kasashen musulmi su yi amfani da karfinsu wajen dakile laifukan gwamnatin sahyoniyawan a Gaza.

Dole ne a daina kisan kare dangi a Gaza ba tare da wani sharadi ba inji shi.

Da yake tabo batun goyon bayan da sojojin Amurka suke ba wa sojojin mamaya na Isra’ila a yakin da suke yi na tsawon watanni a Gaza, ya kara da cewa, “Ya kamata Amurkawa su dakatar da tallafin makamai da suke ba wa gwamnatin sahyoniyawan.

A nasa bangaren, ministan harkokin wajen kasar Iraki ya bayyana ziyarar ta Bagheri Kani a Iraki a matsayin ci gaba a huldar kasashen biyu masu makwabtaka da juna.

Hussein ya kuma jaddada wajabcin gudanar da shawarwari domin lalubo bakin zaren warware tashe-tashen hankula a yankin.

“Ba ma bukatar tsagaita wuta na wucin gadi amma ta dindindin a Gaza, inji ministan harkokin wajen kasar Iraki Fuad Hussein.

Muna goyon bayan tsagaita bude wuta mai dorewa a Gaza, in ji shi, ya kuma kara da cewa, “Halin tsaro a yankin na ci gaba da tabarbarewa, muna kuma gargadi game da yaduwar yakin, musamman game da hare haren Isra’ila a kudancin kasar Labanon

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments