Firaministan Qatar ya ce, duk wani mataki da za’a dauka game da kawoi kartshen yakin Gaza dole ya faro daga kafa kasar Falasdinu mai cin gashin kanta.
Bayan yarjejeniyar tsagaita wuta da MDD ke marawa baya, da kwamitin sulhu ya amince da ita, firaministan Qatar ya jaddada bukatar samar da mafita ta dindindin ga hare-haren da Isra’ila ke ci gaba da yi a yankin Zirin Gaza da aka yi wa kawanya maimakon “matakan wucin gadi.”
Sheikh Mohammed Al Thani ya bayyana hakan ne a yayin wani taron manema labarai na hadin gwiwa da sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken a birnin Doha.
Babban jami’in diflomasiyyar na Amurka, a nasa bangaren, ya yi jawabi kan martanin da Hamas ta mayar kan shirin tsagaita wuta da MDD ke marawa baya.
M. Blinken ya ce wasu gyare-gyaren da kungiyoyin Falasdinawan suka nema zasu samu, amma wasunsu ba zasu samu ba.
Sakataren harkokin wajen Amurka ya gana da firaministan Qatar inda suka tattauna batun tsagaita bude wuta a zirin Gaza bayan da kungiyoyin Falasdinawa na Hamas da ta Islama Jihad suka mikawa masu shiga tsakani na Qatar da Masar martani kan yarjejeniyar da Majalisar Dinkin Duniya ke marawa baya.
Tuni dai kungiyar Hamas ta yi marhabin da kuri’ar da kwamitin sulhun ya kada na amincewa da kudurin da ke goyon bayan tsagaita bude wuta, Sai dai Hamas ta ce dole ne a biya bukatunta da suka hada da tsagaita bude wuta na dindindin da kuma janye sojojin Isra’ila gaba daya daga Gaza.