Majalisar Dinkin Duniya, ta sanya Sojojin Sudan da dakarun RSF cikin jerin ‘’ ‘yan ta’adda saboda kisa da raunata kananan yara da kuma kai hare-hare a makarantu da asibitoci.”
Rahoton na majalisar kan ”yara a yankunan da ke fama da riciki” ya bayyana cewa tashe-tashen hankula da yara suke fuskanta a wuraren da ke fama yaki ya kai matakin kololuwa a shekarar 2023 musamman a Gaza da Sudan.
“A shekarar 2023, cin zarafin kananan yara a wuraren da ke fama da tashe-tashen hankula ya yi tsanani sosai, inda aka samu karin kashi 21 cikin dari a manyan laifuka,” in ji rahoton Sakatare-Janar na MDD Antonio Guterres, wanda aka shirya wallafa shi yau Alhamis.
MDD ta tabbatar da cin zarafin yara 30,705 a bara, wadanda suka hada da kashe yara 5,301 tare da raunata 6,348, sannan an hana yara 5,205 samun agajin jin kai kana an yi garkuwa da 4,356.
An bayyana ukubar da yara suka shiga a bara da mafi muni.
A shekarar 2023, ”Yara sun fuskanci wahalhalu iri daban-daban da kuma munanan tashe-tashen hankula da ke tattare da rashin mutunta hakkin yara, musamman hakkin rayuwa,” in ji rahoton.