Hukumar lafiya ta Duniya WHO ta bada sanarwan cewa gwamnatin HKI ta jefa yara kanana yan kasa da shekaru 5 kimani 8000 a gaza cikin tsananin yunwa wanda zai iya san su rasa rayukansu.
Tashar talabjin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto babban sakaren hukumar WHO Tedros Adhanom Ghebreyesus yana fadar haka, ya kuma kara da cewa, akwai yara kimani 1,600 wadanda suke fama da rashin abincin mai gina jiki da ya dace da su kuma suna iya mutuwa a wani lokaci daga yanzu saboda hakan.
Kafin haka kungiyar UNICEF mai kula da yara ta MDD ta bayyana cewa akwai yara kimani 3,000 a gaza wadanda suna iya mutuywa a gaban iyayensu a Gaza saboda rashin abinci mai gina jikin da ya dace da su. Hka ta toshe dukkan hanyoyin shigar da abinci zuwa gaza tun fiye da watan gudan day a gabata.
Tun cikin watan da ya gabata ne sojojin HKI suka hana abinci da magunguna da kuma dukkan bukatun rayuwa na Falasdinawa shiga gaza. Kuma akwai yiyuwarn mutane kimani miliyon guda zasu rasa rayukansu a gaza saboda yunwa.