Gaza: Kungiyar Hamas Ta Sha Alwashin Ci Gaba Da Nuna Turjiya A Yakin Da Take Fafatawa Da HKI

Shugaban bangaren siyasa na kungiyar Hamas wacce take gwagwarmaya da sojojin HKI, Isma’ila Haniyya ya bayyana cewa kungiyarsa ba zata mika kai ga HKI saboda

Shugaban bangaren siyasa na kungiyar Hamas wacce take gwagwarmaya da sojojin HKI, Isma’ila Haniyya ya bayyana cewa kungiyarsa ba zata mika kai ga HKI saboda kubutar da fursinoni 4 daga kungiyar da ransu da ta yi ba.

Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto Haniyya yana fadar haka bayan hare hare mafi muni wadanda sojojin HKI suka kai garin Nuraita inda suka kashe Falasdinawa akalla 210 sannan wasu 400 suka ji rauni a cikin wata makaranta na MDD.

Haniyya ya bayyana cewa Hamas zata dakatar da yaki nem kawai idan HKI ta yarda da bukatun kungiyar na samarwa Falasdinawa tsaro da kuma janyewar sojojin HKI daga Gaza da kuma sake gina shi.

Haniyya ya kara da cewa, HKI ta rika ta fadi a wannan yakin, a fagen fama, da siyasa da mutunci. Ya ce kungiyar Hamas a shirye take ta ci gaba da yaki, har zuwa bbiyan bukatunta da kuma nasara a kan HKI.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments