Gaza : Iran, Ta Yi Kakkausan Suka Kan Goyan Bayan Da Amurka Da Turai Suke Baiwa Isra’ila

Iran, ta yi kakkausan suka kan ci gaba da goyan bayan da Amurka da Turai suke baiwa Isra’ila. Da yake wannan suka Kakakin ma’aikatar harkokin

Iran, ta yi kakkausan suka kan ci gaba da goyan bayan da Amurka da Turai suke baiwa Isra’ila.

Da yake wannan suka Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Nasser Kan’ani, ya bayyana cewa dakatar da wannan goyon baya ne kadai hanyar da za ta kawo karshen bala’in da ke ci gaba da faruwa a yankunan Falasdinawa da Isra’ila ta mamaye.

A cikin wata sanarwa da aka yi ta dandalin sada zumunta na X a ranar Juma’a, Kan’ani ya yi tsokaci kan ci gaba da tashe-tashen hankula da wahalhalun da dubban daruruwan fararen hula suke fuskanta a Gaza, yana mai jaddada bukatar a gudanar da bincike kan wadannan batutuwa.

Ya yi nuni da cewa zaluncin da “gwamnatin wariyar launin fata ta Isra’ila” ta yi kan fararen hula Falasdinawa, musamman mata da kananan yara, abin takaici ne.

Kan’ani ya ce, “Bai isa a yi magana kawai a kan wadannan ayyukan ba; Ana bukatar cikakken dakatar da goyon bayan Amurka da Turai ga gwamnatin Isra’ila don kawo karshen wannan bala’i mai radadi a kan al’ummar Falastinu.”

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments