Bahrain, Ta Aike Da Sako Ga Iran, Na Neman Daidaita Alaka

Kasar Bahrain, ta aike wa da Iran sako na neman daidaita alaka a tsakaninsu. Wani jami’in gwamnatin Iran ya ce Bahrain ta aike da sako

Kasar Bahrain, ta aike wa da Iran sako na neman daidaita alaka a tsakaninsu.

Wani jami’in gwamnatin Iran ya ce Bahrain ta aike da sako ga Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta hanyar kasar Rasha don daidaita dangantakar da ke tsakaninta da kasar bayan shafe fiye da shekaru takwas ana yi.

Mohammad Jamshidi mataimakin babban hafsan hafsoshi kan harkokin siyasa na shugaban kasar Iran ya bayyana hakan a wata hira da aka yi da shi ta gidan talabijin a ranar Juma’a.

Dama a makon jiya Sarki Hamad bin Isa Al Khalifah ya bayyana yayin wata ziyararsa a kasar Sin cewa, Bahrain na kokarin maido da huldar jakadanci da makwabciyarta Iran.

“Muna aiki don maido da huldar diflomasiyya da Iran a matsayin makwabciyarta,” in ji shi.

Sarkin ya ce kasarsa na maraba da goyon bayan kasar Sin ga kokarin da ake yi na samar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a yammacin Asiya.

Kasar Bahrain dai ta bi Saudiyya wajen yanke huldar diflomasiyya da Iran a ranar 4 ga watan Janairun 2016, bayan da masu zanga-zangar a Iran, wadanda suka fusata da hukuncin kisa kan fitaccen malamin Shi’a nan Sheikh Nimr Baqir al-Nimr da gwamnatin Saudiyya ta yi, suka kai farmaki kan ofishin jakadancinta da ke Iran.

Iran da Saudiyya sun cimma yarjejeniya a birnin Beijing na kasar Sin a watan Maris din shekarar 2023 don maido da huldar jakadanci da bude ofisoshin jakadanci da ofisoshin jakadancinsu.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments