Masu zanga-zangar sun shiga ginin ofishin jakadancin Isra’ila a San Francisco

Daruruwan masu zanga-zangar  adawa day akin kisan kare dangi da Isra’ila take kaddamarwa kan al’ummar Falastinawa mazauna Gaza, sun mamaye ginin karamin ofishin jakadancin Isra’ila

Daruruwan masu zanga-zangar  adawa day akin kisan kare dangi da Isra’ila take kaddamarwa kan al’ummar Falastinawa mazauna Gaza, sun mamaye ginin karamin ofishin jakadancin Isra’ila da ke San Francisco a ranar Litinin, ayyin da ‘yan sanda suka yi amfani da karfi wajen aukawa kan masu zanga-zangar, tare da kame wasu daga cikinsu.

Zanga-zangar tana a matsayin ci gaba ne na bacin rai da mutane da dama ‘yan kasar Amurka suke nunawa kan kisan kiyashin da Isra’ila take ci gaba da yi a Gaza.

Babban kwamishinan ‘yan sanda an San Francisco Jesse Cruz ya bayyana cewa mutane da dama ne suka shiga cikin ginin ofishin jakadancin na Isra’ila.

Yayin da zanga-zangar ta kara ta’azzara, ‘yan sanda sun yi gargadi ga masu zanga-zangar, inda suka shawarce su da su fice daga harabar ko kuma a kama su, sai masu zanga-zangar sun yi zaman dirshan a cikin harabar ofishin jakadancin na Isra’ila har sai da ‘yan sanda suka yi amfani da karfi wajen fitar da su.

Wasu daga cikin masu zanga-zangar sun manna takardua  kan ginin ofishin an Isra’ila da aka rubuta cewa, kiyayya da zaluncin sahyuniya bay a nufin kiyayya da addinin yahudanci.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments