Iran : Batun Falasdinu Shi Ne Na Farko Mafi Mahimmanci A Duniyar Musulmi_ Jagora

Jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran, Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya ce Falastinu ita ce batu na farko kuma mafi muhimmanci a duniyar musulmi.

Jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran, Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya ce Falastinu ita ce batu na farko kuma mafi muhimmanci a duniyar musulmi.

Jagoran ya bayyana hakan ne a jawabin da ya gabatar ga dimbin al’ummar kasar da suka taru a hubbaren marigayi Imam Khumaini da ke kudancin birnin Tehran yau Litinin a zagayowar cika shekaru 35 da rasuwar marigayi Imam Khumaini., wanda ya assasa Jamhuriyar Musulinci ta Iran.

Ayatullah Khamenei ya ce farmakin guguwar Al-Aqsa kan Isra’ila ya zo a daidai lokacin da ya dace da kuma dora gwamnatin sahyoniyawan a kan turbar da za ta kai ga kawar da ita.

Ya kara da cewa, a lokacin farmakin mai lakabin guguwar Al-Aqsa, Falasdinawa sun tura makiya zuwa wani lungu da ba su da hanyar tsira.

Kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta Hamas ta kaddamar da Operation Al-Aqsa Storm a ranar 7 ga Oktoba, 2023, inda ta kutsa cikin yankunan da gwamnatin Isra’ila ta mamaye, ta hanyar kai hare-hare da dama ta sama, da kasa da kuma ta ruwa.

Kungiyar ta ce farmakin na mayar da martani ne ga yadda ake ci gaba da tozarta masallacin Al-Aqsa da ke birnin Quds da ke mamaye da kuma yadda Isra’ila ke ci gaba da zaluntar Falasdinawa a yammacin gabar kogin Jordan da ta mamaye.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments