Iran : Bagheri Kani, Ya Je Lebanon Domin Tattauna Halin Da Ake Ciki A Falasdinu

Ministan harkokin wajen kasar Iran na riko, Ali Bagheri Kani, ya gana da manyan jami’an kasar Lebanon a birnin Beirut yau litinin a ziyararsa ta

Ministan harkokin wajen kasar Iran na riko, Ali Bagheri Kani, ya gana da manyan jami’an kasar Lebanon a birnin Beirut yau litinin a ziyararsa ta farko tun bayan da ya hau wannan sabon mukamin.

Mista Kani ya je ne domin  tattauna halin da ake ciki kan ci gaba da kai hare-haren bama-bamai da Isra’ila ke yi a zirin Gaza da kuma rikicin kudancin Lebanon.

Ministocin harkokin wajen kasashen biyu sun sake nanata sukarsu kan matakin da Isra’ila ke dauka kan al’ummar Palasdinu a Gaza, yayin da suke tattaunawa kan hanyar samar da zaman lafiya a kudancin Lebanon.

Kafofin yada labaran Iran sun ce Mista Kani zai tattauna batutuwan da suka shafi yankin musamman halin da Falasdinu ke ciki.

Ziyarar ta zo ne a daidai lokacin da kungiyar Hizbullah da Isra’ila ke ci gaba da musayar wuta a kan iyakokin kasar a kullum a kudancin kasar Labanon, wanda sannu a hankali ke kamari.

Ziyarar Mr Kani ta zo bayan kalaman shugaban Amurka Joe Biden a ranar Juma’ar da ta gabata kan kawo karshen yakin Gaza.

Mista Biden ya bukaci Hamas da shugabannin Isra’ila da kada su “rasa wannan dama da aka samu” ta neman zaman lafiya.

Taswirar da Mista Biden ya bayar ta hanyar da za a tsagaita wuta ta dindindin da kuma kawo karshen yakin da ya lakume rayukan al’ummar Gaza fiye da 36,400 tare da jikkata sama da 82,400 tun bayan da Isra’ila ta kaddamar da hare-hare a zirin Gaza bayan harin ba zata na Hamas na ranar 7 ga watan Oktoba.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments