Zanga-Zangar Neman Korar Masu Goyon Bayan Haramtacciyar Kasar Isra’ila Daga Kasar Mauritaniya

Al’ummar Mauritaniya sun gudanar da zanga-zangar neman korar jakadun kasashen da suke goyon bayan haramtacciyar kasar Isra’ila daga cikin kasarsu A cikin fusata al’ummar Mauritaniya

Al’ummar Mauritaniya sun gudanar da zanga-zangar neman korar jakadun kasashen da suke goyon bayan haramtacciyar kasar Isra’ila daga cikin kasarsu

A cikin fusata al’ummar Mauritaniya musamman matasan kasar sun fito zanga-zanga, inda suke rera taken tofin Allah tsine da yin Allah wadai da munanan laifukan da yahudawan sahayoniyya suke tafkawa a Zirin Gaza da birnin Rafah.

Masu zanga-zangar sun kuma shirya wani taron gagarumi a gaban ofishin jakadancin Amurka da ke birnin Nouakchott, inda suka bukaci a kori jakadun kasashen da suke nuna goyon baya ga ‘yan mamayar yahudawan sahayoniyya da suke aikata mafi munin ayyukan ta’addanci kan bil’adama.

Yahya Jamil Mansour, mamba a kungiyar Dalibai don yakar kutsawar yahudawan sahayoniyya a kasar Mauritaniya, ya ce: Amurka ce babbar mai hannu a kisan kiyashin da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ke aiwatarwa kan al’ummar Falasdinu, don haka suna jaddada bukatar yanke alaka da duk wata kasa da take goyon bayan ayyukan ta’addancin yahudawan sahayoniyya tare da korar jakadunsu daga Mauritaniya musamman jakadan Amurka.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments