An Fara Rejistar Takarar Shugaban Kasa A Iran

A Iran, yau Alhamis ne aka bude rejistar ‘yan takara a zaben shugaban kasar na maye gurbin shugaban kasar da ya yi shahada a hatsarin

A Iran, yau Alhamis ne aka bude rejistar ‘yan takara a zaben shugaban kasar na maye gurbin shugaban kasar da ya yi shahada a hatsarin jirgin sama mai saukar ungulu.

Za’a ci gaba da rejistar har zuwa ranar 3 ga watan Yunin gobe a ma’aikatar harkokin cikin gidan kasar dake Tehran.

A ranar 28 ga watan Yunin 2024 ne za’a gudanar zaben shugaban kasar.

Kundin tsarin mulkin kasar ne ya tanadi gudanar da zabe cikin kwanaki 50 idan wani shugaban kasar ya rasu ko kasawa ko tsigewa.

Tsohon shugaban kasar Iran Ibrahim Raisi tare da mukarabansa ciki har da ministan harkokin wajen Hossein Amir Abdolahian, sun yi shahada ne a ranar 19 ga watan Mayu yayin wani hatsarin jirgin Helikwabta a kan hanyar zuwa Tabriz da ke arewa maso yammacin kasar bayan sun halarci wani bikin kaddamar da wata madatsar ruwa a iyaka da kasar Azerbaijan.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments