Iran : An Fitar Da Rahoto Na Biyu Game Da Hatsarin Jirgin Shugaban Kasa

A rahoto na biyu wanda kwamitin da sojojin kasar Iran suka kafa don bincike da gano musabbabin faduwar jirgin shugaban kasa a ranar Lahadi 19

A rahoto na biyu wanda kwamitin da sojojin kasar Iran suka kafa don bincike da gano musabbabin faduwar jirgin shugaban kasa a ranar Lahadi 19 ga watan Mayu, ya nuna cewa hatsari ne jirgin yayi.

Kamfanin dillancin labarai Iran press na kasar Iran ya nakalto Gholam-Hussain Esma’ili shugaban ma’aikata a ofishin shugaban kasa yana fadar haka a ranar Laraba. Ya kuma kara da cewa kwamitin ya fidda bayanai na asali wadanda suka shafi faduwar jirgin, kuma nan gaba za’a fidda cikekken bayanin kan hatsarin.

A ranar lahadi 19 ga watan Mayu ne jirage guda ukku, dayansu dauke da shugaban kasa, Ministan harkokin waje, wakilin Jagora a jihar Azarbajan ta gabas, gwamnan Azarbaijan ta gabas, da masu gadin shugaba kasa, matuka jirgi da masu hidima yayi  hatsari a kan hanyarsu ta dawowa Tabriz daga kasar Azarbaijan, inda aka kaddamar da wata madatsra ruwa.

Sanadiyyar wannan hatsarin dai shugaban kasa da dukkan wadanda suke tare da shi sun rasa rayukansu .

Rahoton ya kara da cewa a wannan rahoton na biyu sun yi bincike kan inda suka sami jirgin babba da kuma inda suka sami sauran bangarensa da kuma mutanen da suke cikinsa na nuna cewa jirgin ya doki jikin dotse ne sannan ya fadi kasa.

Share

4 1 vote
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments