Kwamitin Tsaron MDD Zai Gudanar Da Zama Taro Kan Rafah Na Falasdinu

A yau ne kwamitin tsaron Majalisar Dinkin Duniya zai gudanar da zaman taron gaggawa don tattauna halin da ake ciki a birnin Rafah na Falasdinu

A yau ne kwamitin tsaron Majalisar Dinkin Duniya zai gudanar da zaman taron gaggawa don tattauna halin da ake ciki a birnin Rafah na Falasdinu

Kwamitin tsaron Majalisar Dinkin Duniya zai gudanar da wani zaman taron gaggawa, a yau Talata, domin tattauna halin da ake ciki a birnin Rafah da ke Zirin Gaza bayan kisan kiyashin da sojojin gwamnatin mamayar haramtacciyar kasar Isra’ila suka yi a cikinsa.

Majiyoyin diflomasiyya sun shaidawa kamfanin dillancin labaran Faransa cewa: Kwamitin tsaron zai gudanar da zaman taron ne bisa bukatar kasar Aljeriya.

Kuma wani abin lura shi ne cewa: Falasdinawa 45 ne suka yi shahada tare da jikkata wasu da dama, a wani sabon kisan kiyashi da sojojin gwamnatin mamayar haramtacciyar kasar Isra’ila suka aiwatar kan Falasdinawan yankin, bayan da suka kai hare-haren bama-bamai kan sansanin ‘yan gudun hijira da ke arewa maso yammacin birnin na Rafah.

Sansanin dai yana cikin yankunan da a baya sojojin mamayar yahudawan sahayoniyya suka gano cewa yana daga cikin wurare masu aminci, kuma sojojin mamayar ne suka bukaci ‘yan gudun hijirar Falasdinawa su koma wurin, amma ba tare da wata sanarwa ko gargadi ba kan bukatar barin wurin suka yi luguden bama-bamai kan mazauna yankin.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments