Iyalan Shugaban Kasar Iran Ibrahim Ra’isi Sun Mika Sakon Godiya Ga Jagoran Musulunci

Iyalan shahidi Ayatullah Ibrahim Ra’isi sun mika godiyarsu ga Jagoran juyin juya halin Musulunci da al’ummar Iran A cikin bayanin godiya da jinjina da iyalan

Iyalan shahidi Ayatullah Ibrahim Ra’isi sun mika godiyarsu ga Jagoran juyin juya halin Musulunci da al’ummar Iran

A cikin bayanin godiya da jinjina da iyalan shahidi Ayatullah Ibrahim Ra’isi suka aike ga Jagoran juyin juya halin Musulunci sun bayyana godiyarsu ga jagoran juyin juya halin Musulunci mai hikima da kuma jarumtakar al’ummar Iran da suka raini shahidai, bisa la’akari da cewa dukkanin wannan ta’aziyya da juyayi na gaskiya da basira da suka wuce iyakokin Iran sun nuna cewa wani sabon mataki na yunkurin juyin juya halin Musulunci ya riga ya fara, kuma al’ummar Iran suna da nauyi mai girma da tarihi na kiyayewa, da ingantawa da kuma kammala abubuwan da suka gada daga manyan shahidai.

Bayanin ya kara da cewa: A yau Ubangiji madaukaki da buwaya ya daukaka zuriyar Annabi Ibrahim (A.S) da darajar shahada, don haka babu mafita sai hakuri da tsayin daka wajen aiwatar da koyarwar wannan mai girma kuma annabi, domin lokacin hadin kan duniya ya zo don ci gaba da tafarkin manyan annabawa wajen yaki da zalunci da rashin adalci.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments