Ba Wani Sauyi A Irin Goyan Bayan Da Iran Ke Ba Kungiyoyin Gwagwarmaya_ Mokhber    

Shugaban riko na kasar Iran, Mohammad Mokhber ya ce ba za a samu wani sauyi ba a irin goyon bayan da kasar ke bai wa

Shugaban riko na kasar Iran, Mohammad Mokhber ya ce ba za a samu wani sauyi ba a irin goyon bayan da kasar ke bai wa kungiyoyin gwagwarmaya ba, musamman na Falasdinu, bayan shahadar shugaba Ebrahim Raeisi.

Mokhber ya bayyana hakan ne yayin wata tattaunawa ta wayar tarho da babban sakataren kungiyar gwagwarmayar Islama ta Islamic Jihad, Ziad al-Nakhalah.    

Ya ce, shugaba Raeisi da ministan harkokin wajen kasar Hossein Amir-Abdollahian, wadanda suka rasa rayukansu a wani hatsarin jirgin sama mai saukar ungulu a makon da ya gabata, sun damu matuka game da batun hakkokin Falasdinawa.

Mokhber ya kara da cewa: “Tsarin Jamhuriyar Musulunci ta Iran wajen tallafawa ‘yan gwagwarmaya, ba za su canza ba saboda sauyin mutane.”

Ya kuma bayyana tsayin daka a matsayin hanya mafi inganci don tinkarar laifuffukan da Isra’ila ke yi.     

A nasa bangare shugaban kungiyar ta Hamas, ya ce shahiddan na Iran, sun kare hakkin Falasdinawa a tarurrukan yanki da na kasa da kasa kuma sun yaba da tsayin dakan da suka yi wajen kalubalantar mamayar Isra’ila.

M. Nakhalah ya jajantawa gwamnati da al’ummar Iran, yana mai cewa kasar za ta shawo kan wannan bala’i sakamakon kwararrun jami’anta da kuma al’ummarta masu neman sauyi.

Ya kara da cewa “Shahidi Raeisi da Shahidi Amir-Abdollahian a ko da yaushe a sahun gaba wajen kare muradun al’ummar Iran da kuma goyon bayan tsayin daka.”

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments