Shugaban Rikon Kwarya A Kasar Iran Ya Jaddada Aniyar Iran Na Tallafawa kungiyoyin Falasdinawa

Shugaban rikon kwarya a kasar Iran ya jaddada cewa: Tsarin Iran na tallafawa kungiyoyin gwagwarmaya ba zai canza ba Shugaban rikon kwarya da ke tafiyar

Shugaban rikon kwarya a kasar Iran ya jaddada cewa: Tsarin Iran na tallafawa kungiyoyin gwagwarmaya ba zai canza ba

Shugaban rikon kwarya da ke tafiyar da harkokin shugabancin kasar Iran Muhammad Mokhber ya jaddada shirin Jamhuriyar Musulunci ta Iran na ci gaba da goyon baya ga tsayin dakar al’ummar Falastinu da neman hakkokinsu wanda marigayi shugaban kasa Sayyid Ibrahim Ra’isi da ministan harkokin wajensa Hossein Amir Abdollahian suka tafi a kai, yana mai jaddada cewa: Tsare-tsaren Jamhuriyar Musulunci ta Iran na asali sun ginu ne kan tallafawa kungiyoyin gwagwarmaya musamman kungiyoyin gwagwarmayar Falasdinawa kuma manufofi ne da ba zasu taba canzawa ba. Mokhber ya jaddada hakan ne a zantawarsa da babban sakataren kungiyar Jihadul-Islami Ziyad al-Nakhalah ta hanyar wayar tarho, inda Muhammad Mokhbir ya nuna jin dadinsa ga juyayi da alhinin Ziyad al-Nakhalah ya yi ga gwamnati da al’ummar Iran biyo bayan shahadar Shugaban kasar Iran Ibrahim Ra’isi da mukarrabansa.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments