Burkina Faso : An Kara Wa Sojojin Dake Mulki Wa’adin Shekaru Biyar

Gwamnatin mulkin soji ta Burkina Faso za ta ci gaba da mulki har nan da shekaru biyar masu zuwa bayan mahalarta taro kan makomar kasar

Gwamnatin mulkin soji ta Burkina Faso za ta ci gaba da mulki har nan da shekaru biyar masu zuwa bayan mahalarta taro kan makomar kasar sun bayar da shawarar komawa kan mulkin dimokuradiyya zuwa watanni 60 daga watan Yuli mai kamawa.

Sabon tsarin, wanda shugaban mulkin sojin Burkina Faso Ibrahim Traore ya sanya wa hannu, ya nuna cewa za a mayar da mulki hannun gwamnatin farar-hula cikin watanni 60 daga ranar 2 ga watan Yuli.

Sabuwar dokar ta amince Ibrahim Traore ya tsaya takara a zaben da za a gudanar.

Wannan shawara na cikin wata takarda da mahalarta taron suka amince da ita, wadda za ta kasance wani sabon tsari na gudanar da mulki a kasar.

Sojojin Burkina Faso sun kwace mulki a shekarar 2022 sannan suka yi alkawarin gudanar da zabe a watan Yulin wannan shekarar domin komawa turbar dimokuradiyya, sai dai sun ce shawo kan rashin tsaron kasar shi ne babban abin da suka sanya a gaba.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments