Majalisar Dokokin Kasashen Larabawa Ta Bukaci A Dakatar Da Yaki A Gaza

Shugaban majalisar dokokin kungiyar kasashen Larabawa ya bukaci a tsagaita budewa juna wuta  a gaza da gaggawa. Kamfanin dillancin labaran IRNA na kasar Iran ya

Shugaban majalisar dokokin kungiyar kasashen Larabawa ya bukaci a tsagaita budewa juna wuta  a gaza da gaggawa.

Kamfanin dillancin labaran IRNA na kasar Iran ya nakalto Adil Al-asumi shugaban majalisar dokokin kungiyar kasashen larabawa yana fadar haka a taron majalisar dokokin kasashen larabawan da aka gudanar a cibiyar kungiyar dake birnin Alkahira na kasar Masar.

Al-asumi ya yi ishara ga kisan kare dangi da kuma korar Falasdinawa daga wuri zuwa wuri a cikin Gaza, har’ila yau da kuma  tallafin makamai wadanda gwamnatin Amurka take bawa HKI a matsayin musibun da suka sami Falasdinawa a cikin watanni fiye da 7 da suka gabata.

Kungiyar ta kira taron na jiya Asabar ne don tattauna batun ci gaba da kisan kiyashin da sojoji HKI suke yi wa Falasdinawa a Gaza.

Labarin ya kara da cewa kwamiti na musamman don Falasdinu a majalisar ya yi kira da a kawo karshen yaki a Gaza da gaggawa sannan ya yi kira ga kasashen duniya su shigo tsakani don kawo karshen kisan kiyashin da sojojin HKI suke yi a gaza.

Tun ranar 7 ga watan Octoban shekarar da ta gabata ce sojojin HKI suka fara luguden wuta a kan Gaza, kuma ya zuwa yanzu sun kai Falasdinawa akalla 35,000 ga shahada a yayinda wasu 80000 suka ji rauni.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments