Babbar kotun Majalisar Dinkin Duniya ta umarci Isra’ila ta dakatar da hare-haren da take kai wa a yankin Rafah na Gaza ba tare da bata lokaci ba.
Kotun ta kuma ce shiga tsakani na da matukar muhimmanci domin kare rayuwar Falasdinawa.
Afirka ta Kudu ce dai ta nemi kotun ta umarci Isra’ila da ta dakatar da hare-haren soji kan birnin Rafah dake Kudancin Gaza.
Bukatar baya-bayan nan ta bayyana cewar rokon da aka yi na farko da matakin da Hague ta dauka bai isar ba wajen magance “Munanan hare-haren soji kan ‘yan gudun hijirar Gaza.”
Afirka ta Kudu ta bukaci kotun da ta umarci Isra’ila ta janye daga Rafah; ta dauki matakan tabbatar da jami’an MDD, ma’aikatan jinkai da ‘yan jaridu sun shiga yankin Gaza.
Dama a watan Janairu, alkalai sun umarci Isra’ila da ta nisanci kisa, rushe gine-gine da duk wani nau’i na kisan kiyashu a Gaza.
Sannan a umarni na biyu a watan Maris, kotun ta ce dole ne Isra’ila ta dauki matakan inganta ayyukan jinkai a Gaza, ciki har da bude karin hanyoyin kai kayan abinci, ruwa, man fetur da sauran kayayyaki.
To saidai a ko yaushe Isra’ila kan yin fatali da hukunce-hukunacen kotun.
Kakakin gwamnatin Isra’ila ya ce babu wani mai iko a doron kasa da zai hana ta kare mutanenta da kuma murkushe Hamas a Gaza.