Mukaddashin Ministan Harkokin Wajen Kasar Iran Ya Ce Kasar Zata Ci Gaba Da Kyautata Dangantaka Da Kasashen Duniya

Mukaddashin ministan harkokin wajen kasar Iran Dr Mohammad Bakiri Kani a cikin tattaunawa ta wayar tarho da tokwarorinsa na kasashen da dama ya bayyana cewa

Mukaddashin ministan harkokin wajen kasar Iran Dr Mohammad Bakiri Kani a cikin tattaunawa ta wayar tarho da tokwarorinsa na kasashen da dama ya bayyana cewa kasar Iran zata ci gaba da kyautata dangantaka da kasashen duniya kamar yadda marigayi Dr shahid Amir Hussain Abdullahiyan ya saba.

Kamfanin dillancin labaran IRNA na kasar Iran ya nakalto Kani yana cewa dukkan yarjeniyoyi da aka cimma tsakanin kasashe daban daban a duniya da kasar Iran za’a ci gaba da aiwatar da su a bangarorin biyu.

Ministan ya kara jaddada cewa babu wani sauyi da za’a samu a cikin dukkan yarjeniyoyi da aka cimma da kasar Iran a zamanin marigayi Shahid Ayatullahi Dr Ibrahim Ra’esi.

Kani ya sami damar tattaunawa da tokwarorinsa na kasashen Qatar, Saudia, Jordan, Turkiya, da mukaddashin ministan harkokin wajen Chian, inda suka gabatar da ta’aziyasu gareshi ga kuma mutanen Iran dangane da shahadar Sayyid Ra’isi da Dr Abdullahiyan da wadanda suke tare da su. Sauran kasashen sun hada da Umman, Azarbaijan, Aljeriya, Sabia.

A ranar lahadi 19 ga watan Mayu ne shugaban kasar Iran Sayyid Ibrahim Ra’isi tare da ministan harkokin wajensa Hussain Amir Abdullahiyan da wadanda suke tare da su suka rasa rayukansu sanadiyyar faduwar jirgin saman da ke dauke da su a kan hanyarsu ta dawowa daga kasar Azarbaijan inda suke yi bukin bude madatsar ruwa wacce kasashen biyu suka gina.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments