Mai Shigar Da Kara A Kotun Kasa Da Kasa Ya Bukaci Fitar Da Sammacin Kama Benjamin Netanyahu

Mai shigar da kara a kotun da ke hukunta manyan laifuka a duniuya da ke birnin Hague ta ICC ya nema fitar da sammacin kama

Mai shigar da kara a kotun da ke hukunta manyan laifuka a duniuya da ke birnin Hague ta ICC ya nema fitar da sammacin kama fira ministan gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila Benjamin Netanyahu

Mai shigar da kara na kotun da ke hukunta manyan laifuka ta duniya ICC, Karim Khan ya bukaci kotun ta kasa da kasa da ta fitar da sammacin kama Fira ministan gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila Benjamin Netanyahu da ministan tsaronsa Yoav Galant da kuma shugaban kungiyar Hamas a Gaza Yahya Sinwar, da Muhammad Al-Deif, babban kwamandan rundunan shahidan Izzuddeen al-Qassam, bangaren sojin kungiyar Hamas da kuma shugaban kungiyar ta Hamas Isma’il Haniyeh, saboda alhakinsu game da abin da ke faruwa a Gaza.

Duk da irin kura-kuran da matakin ke tattare da shi, musamamman wajen daidaita wanda ake zalunta da wanda ke zartar da zalunci ta hanyar aiwatar da kisan kiyashi kan al’umma, da kuma killace al’umma a yankin da babu ruwa babu abinci, za a iya bayyana shi a matsayin wanda ba a taba ganin irinsa ba, domin wannan shi ne karon farko da wata kungiya ta kasa da kasa ta yi kasadar yin hakan. tare da yin Allah wadai da haramtacciyar kasar Isra’ila, ‘yar lelar Amurka, musamman na fitar da sanarwar kame shugabannin yahudawan sahayoniyya da suke da alhakin gudanar da ayyukan ta’addanci a Gaza, kuma suka shafe sama da shekaru 70 suna aikata bakar siyasar mamaya da musgunawa al’umma a kasarsu ta gado.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments