Wani Matashin Bafalasdine Ya Yi Shahada Tare Da Jikkatan Wasu Na Daban A Sansanin Garin Jenin

Wani matashi ya yi shahada tare da jikkatan wasu na daban sakamakon harin da wani jirgin yakin haramtacciyar kasar Isra’ila ya kai a sansanin Jenin

Wani matashi ya yi shahada tare da jikkatan wasu na daban sakamakon harin da wani jirgin yakin haramtacciyar kasar Isra’ila ya kai a sansanin Jenin

Ma’aikatar lafiya ta Falasdinu ta tabbatar da mutuwar wani matashin bafalasdine tare da raunata wasu biyar na daban, inda aka kai su asibitin gwamnati na Jenin, kamar yadda aka kai wasu uku zuwa asibitin Ibn Sina, sakamakon harin wuce gona da iri da jiragen saman yakin sojin haramtacciyar kasar Isra’ila suka kai kan birnin Jenin.

Majiyar cikin gida ta sanar da cewa, an kai harin ne kan wani gida da ke unguwar Al-Damj a sansanin na Jernin, inda harin ya yi sanadin jikkatan Falasdinawa biyar.

Rundunar ‘yan sandan haramtacciyar kasar Isra’ila ta ce matashin da aka kashe mai suna Islam Khamaysa, ana zarginsa da hannu a kai hari kan matsugunin yahudawan sahayoniyya ‘yan kaka gida na Hermish da ke arewacin garin Tul-Karam.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments