Al-Adu Da Ci Gaban Addinin Musulunci A Tarihi 28

28-Assalami alaikum masu sauraro barkammu da warhaka, barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na Al-Adu da ci gaban addinin musulunci a tarihi, shiri wanda

28-Assalami alaikum masu sauraro barkammu da warhaka, barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na Al-Adu da ci gaban addinin musulunci a tarihi, shiri wanda yake kawo maku irin ci gaban da masana a tsawon tarihin addinin musulunci suka kawo na ci gaba a dukkan bangarorin ilmi a doron kasa tun bayyanar addinin musulunci har zuwa yau, wanda ni tahir amin nake kawo maku sau guda a ko wani mako. Da fatan masu sauraro zasu kasance tare da mu acikin shirimmu na yau.

///… Madallah, masu sauraro idan kuna tare da mu a cikin shirimmu da ya gabata mun ci gaba da kawo maku ayyukan malamai likitoci masana ilmin cututtuka da magungunasu da dukkan abinda ya shafi ilmin kiwon lafiya a cikin musulmi bayan bayyanar addinin musulunci.

Mun karasa magana danganeda Abu Ali Sani, inda muka yi maganar muhimmancin littafansa hatta a karnuna bayansa, musamman a kasashen Turai bayan an tarjamasu zuwa harshen Laten, mun bayyana cewa, sun maida littafin Kanoon Fttibbi” na Ibn Sina a matsayin littafin koyon aikin likitanci na asali a Jami’o’insu har zuwa karnuka da dama. Sannan mun bayyana cewa yana da wasu littafai a ayyukan likitanci da wasu fannonin ilmin.

A cikin ilmin falsafa mun bayyana cewa yana da littafi mai suna “shefa” a fannin falsafa. Da wasu da dama.

Daga nan sai muka fara maganar wani likita babba suna Isma’il Jarjani wanda ya tashi a garin Jarjar na yankin Golistan a arewacin kasar Iran a yanzu.

An haifi Sayyid Isma’ila  dan Hussain muhammad Jarjani a girin Jarjar na arewacin kasar Iran a lardin Golistan a halin yanzu, ya shahara da suna Isma’il Jarjani.

Ismail ya hada zamani da Khawarizmi kuma ya rasu a shekara 531 Hijiri a garin Maru na yankin Khurasan.

Wani abinda ya bambanta likitocin da muka yi maganarsu a baya, shi ne su sun yi rubece rubucensu ne da harshen larabci, amma likita na farko da ya rubuita littafai da harshen Farisanci shi ne Isma’ila Jarjani.

Don haka rubuce rubucen Isma’il sune asasin rubuce rubucen ilmin likitanci da harshen Farisanci.

Littafinsa mai suna (ذخیره خوارزمشاهی ) wani kundi ne dangane da ilmin likitanci da harshen farisanci. Littafin ya yi magana dangan da sanin cututtuka, sanin magunguna, sanin tsirrai na magunguna, da kuma bangare babba daga cikinsa don sanin asalin yanda za’a maganin cututtuka.  

Har’ila yau yana ishara ga tsabtar jiki, da ka’idojin cin abinci, da kuma wasu al-amura da suka shafi kiwon lafiya, wanda yakamata mai son lafiyar jikinsa ya kiyasu a tsawon shekara.

Yayi magana da kuma bayani kan daukar jini, da tsbatar hakora, da wasu al-amura da dama.

Girman littafin ya kai mujalladai 10, sannan yana da amfani sosai, saboda haka ne aka tarjama shi zuwa wasu harsuna da suka hada da harshen Ibranci, ko harshen yahudawa.

A shekara ta 506 HK, Jarjani ya takaita littafinsa (ذخیره خوارزمشاهی ) Zakhire Khawarizim Sha, sannan  ya bada shi kyauta ga Sarkin Khawarizim wanda saboda shi ya rubuta littafin tun asali. Saboda shi likitansa ne.

Banda wannan Jarjani yana da wani littafi mai suna ‘Yade Gar” wanda shi ma ya tattara wasu bayanai dangane da ilmin likitanci da magunguna.

Kamar yadda muka gani, a shirye shiryen da suka gabata, malamai masana musulmi daga dukkan kusruwowin daular musulunci sun gabatar da ilmi da ci gaba ga duniya a fannoni da dama. A kasashen Siriya da Masar ma malamai masana da dama sun kawo ci gaba a bangren ilmin kiwon lafiya, likiutanci da magunguna ga duniyar musulmi.

Akwai ibn Nafis wanda aka fi saninsa da Alkurashi a cikin larabawa, masanin ilmin fikihu sanenne kuma marubuci, yana da bincike cikin ilmin likitanci da kiwon lafiya.

An haifi ibn Nafis a birnin Dameshk na kasar Siriya sannan ya koyi aikin likitanci a babban asbitin birnin. Bayan ya kammala karatu ya je kasar Masar inda ya fara aikin karantarwa da kuma likitanci. Sannan saboda korewarsa ya rike mukamai masu muhimmanci da dama a aikin kiwon lafiya.

Saboda haka ya yi amfanida da mukaman da ya samu inda ya fara rubuta wani littafi wanda ya sanya masa suna “Ashamil fi sina’ati tibbiyah” wanda ya kasance kundi babba da ya shafi ilmin likitanci da kiwon lafiya.

An kiyasta cewa, kundin zai kai mujalladai 300. Amma ibnu Nafis ya rubuta mujalladai 80 daga cikinsu. An tattara wasu daga cikin mujalladan littafin a cikin mujalladai 9, ammam daya ne kawai wanda ya rubuta da hannunsa.

Sannan, ibn Nafis yayiwa littafai da rubuce rubuce da dama sharhi. Dangane da cututtukan ido yayiwa littafin- Masa’il Fit Tibbi- Na Hunain dan Ishak sharhi.  

Sharhi da kuma Khulasar, wato takaitaccen littafin Kanoon na Ibnu Sina, wanda ibn Nafis ya yi, shi ne littafin da ake fi karatunsa a wannan fannin. Banda haka, yayiwa littafin Kanoon na Ibn Sina gaba dayansa sharhi.

Daga nan sai Ibn Nafis ya rubuta sharhi daban game da ilmin halittar dan adam. Inda a cikin sa yayi maganar jujjuyawar jini a cikin jijiyoyin dan adam, ya bayyana hakan da kimanin karnuka 3, kafin turawa su gano shi. A binciken da ya gudanar ya bayyana cewa, ra’ayin Galenw dangane hakan kuskure ne. Inda yake cewa jina yana kwarara daga bangare guda na zuciya zuwa dayan bangaren.

Amma ibn Nafis ya gano cewa jini daga ciki ta dama, yake shiga jijiyar jini sannan ya shiga huhu, sannan yi fita dauke da iska, (oxigen) ya shiga wata jijiyar  ya fada bangaren ciki na hagu sannan ya yadu zuwa sauran jikin mutum. Don haka ibn Nafis ya bayyana yanda halattar jikin mutum yake da ilmi ba caci fadi ba. Ta hanyar bincike ya gano hakan. Ya kuma kara da cewa ciki ta hannun hagu yafi ciki ta hannun dama girma. Ya gano haka kafin Likitan Italiya Miguel Ceruto ya bayyana haka.

Don haka Ibn Nafis, da Farabi da Ibn Sina da wasu liktoci musulmi da dama, sun dara Galen sanin al-amura da suka shafi aikin likitanci.

Daga karshe muna iya cewa, ibn Nafis yana daga cikin likitoci wadanda suka gano al-amura masu muhimmanci a ilmin likitanci a tarihin bil’adama.

Saboda haka, ake kiransa Galen da zamanin musulmi, don ya gabatar da bincike mai yawa ya kuma gano ilmi mai yawa dangane da ayyukan kiwon lafiya da aikin likitanci a tarijin dan’adam.

Ibnu Nafis ya gudanar da mafi yawan rayuwarsa a birnin Alkahira na kasar Masar sannan a shekara ta 687 M ya rasu a birnin Alkahirah.

Sannan kafin rasuwarsa, ya bada kyautar gidansa da kuma dakin ajiyar littafansa ga asbitin Mansuri da ke birnin Alkahira.

Yanzun kuma sai wani masanin wanda ake kira Muhzzibud Deen  Dakhwar daya daga cikin fitattun masana ilmin likitancin dan kasar Siriya, da kuma masar wanda ya rayu a karni na 7 kamariyya. Dakhawar ya na da talobai da dama a kasar Siriya a kuma birnin Damesh babban birnin kasar. Kafin rasuwarsa da kadan ya gina makaranta ta musamman don koyon aikin likitanci. An bude wannan makarantar a shekara 628 hijia kuma makarantar ci gaba gaba har zuwa shekara 820 hijira tana horas da daliban ilmin likitanci.

Har’ila yau an yi wani likitan a kuma masanin ayyukan jiya da magunguna a cikin karni ta 7 kamariyya shi ma, wanda ake kira Ibn Quf, ibnu Quf yana daga cikin daliban Ibn Nafis wanda muka yi maganarsa a baya, a birnin Demash na kasar Siriya.

Ibn Quf ya kware a ayyukan tiyata, kuma ya rubuta wani littafi dangane da ayyukan tiyata kadai, littafin yana da matukar muhimmanci ga wadanda suke karatu ilmin aikin tiyata.  

Littafin mai suna (العُمدةُ فی صَناعة ِ الجَراحة) yana maganar hanyoyin tiyata daban daban, in banda tayatar bangaren cututtukan ido. Wannan kuma saboda a zamanin ana daukar ilmin cututtukan ido, baya cikin ilmin likitanci.

Ibn Quf yayi ayyuka da dama, a wannan bangaren, daga ciki ya shahara bayani kan ilmin jijiyoyin jini da kuma jujjuyawar jini a cikin zuciya. Ya gano dukkansu, karnuka kafin a samar da microscop, sannan karni 4 kafin Malpighian ya bayyana shi a kasashen turai.

Har’ila yau musulmi sun yi fice a aikin cututtukan ido ma, sun libuta littafai na musamman wadanda suka kebe ilmin. Muna iya cewa dukkan masana ilmin likitanci sun ware wani bangare a cikin wallafe wallafensu don magana a kan ilmin cututtukan ido. Kamar sauran cututtka a wannan bangaren ma, sun samar da sabbin ilmi da kuma ci gaba. Daga ciki sun gano kuma sun bambanta cututtukan ido daban daban, da kuma magungunan da suka dace da ko wace cuta. Haka ma sun samarda hanyoyin tiyatar idano, da nau’o’in magunguna idanu wadanda suka hada da na ma’adinai, ko tsirrai ko kuma na dabbobi. Sun gano hanyoyin fiddaruwan da ke taruwa a cikin idanu a wasu lokuta su hana gani .

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted