Kungiyar Hamas wacce take iko da Zirin Gaza ta musanta zargin haramtacciyar kasar Isra’ila dangane da cewa kungiyar ta maida Asbitin Al-Ahli Arab a matsayin barikin soje don halattawa kanta kai hare hare kan asbitin .
Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta nakalto majiyar Hamas na fadar cewa asbitin Arab Al-Ahli da ke Gaza shi ne asbiti tilo wanda yake aiki a yankin, don haka Isra’ila tana son ta kai hare hare ta kuma wargaza asbitin tare da wannan zargin.
Hamsa ta yi kira ga kasashen duniya da kungiyoyin kare hakklin bil’adama su yi wani abu don kare al-ummar falasdinu a gaza.
Kungiyar har’ilayau ta musanta zargin Isra’ila na cewa tana amfani da daya daga cikin gine ginen da ke cikin asbitin a matsayin wurin azabtar da Falasdinawa wadanda suka sabawa ra’ayinta. Ta ce wadannan zarge zarge karyace, tana son ta yi amfani da su don rusa asbiti tilo dake Gaza wanda zai kara jefe falasdinawa cikin karin musiba banda wadanda take cikinsu.
A ranar Alhamis ce rundunar sojojin Isra’ila wacce ake kira Shin Bet ta fitar da wata sanarwan tana zargin kungiyar Hamas da amfani da wani gini a cikin asbitin Al-Ahli Araba a gaza saboda ayyukan soje da kuma wurin azzabtar da wasu Falasdinawan.. Yahudawan basu gabatar da wata shaida ta tabbatar da wannan zargin ba.