Hukuma mai kula da kafafen yada labarai a kasar Burtania (Ofcom) ta kwace lacicin tashar talabijin ta yan adawar kasar Bahrai da ke birnin Londan saboda yadda tashar take karfafa take kuma kira gay an adawa a kasar su goyi bayan masu adawa a kasar su karfafa matsin lamba ga gwamnatin kasar ko gwamnatin dangin Ali Khalifa saboda takurawan da sukewa mutanen kasar.
Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta nakalto majiyar tashar LualuaTv a ranar Jumma’a ce hukumar OFcOm ta bada sanarwan dakatar da aikin tashar talabijan din.
Amma ofcom ta bayyana cewa kamfanin Shells for Media Productions Limited bai cancanci ya samarwa tashar talabijin din lasisin aiki a kasar Burtania ba. Wannan na faruwa ne dai dai lokacinda gwamnatin sarakunan Ali Khalifa suke dirar mikiya a kan yan adawa a kasar ta Bahrain,suka kuma kama mutane 60 da wani abu, mafi yawansu malaman addini sannan kotunan kasar suka yanke masu hukuncin daurin rai dai sannan wasu kuma kaso na lokaci mai tsawo a gidan yari.
A wani bangare hukumar Ofcom y ace wai ta sami labarai da bayanai da dama wadanda suke goyon bayan kungiyar Hamas ta Gaza wacce gwamnatin Burtania take dauke a matsayin kungiyar yan ta’adda. Sannan wasu na goyon bayan Hizbullah na kasar Lebanon da kuma Islamic Jihad na kasar Falkasdinu wadanda dukkaninsu gwamnatin kasar Burtania tana daukarsu a matsayin kungiyoyin yan ta’adda.
Sun ce sun sami jawani na shugaban kungiyar Ansarullah na kasar Yemen seyyed Abdulmalikk badruddeen Huthi na tsawon minti 45 a shafin takar talabijin ta Lualua tv inda yake magana dangane da cika shekaru 3 ga yakin tufanulaksa ta 23-11-2023. Kan yahudawan sahyoniyya.