Najeriya: Kawancin Atiku Da Obi A Zaben 2027 Zasu Yi Taro A Abuja

Yan takarar shugaban kasa, a zaben ranar 16 ga watan Jeneru na shekara ta 2027 wato Alhaji Atiku Abubakar na Jam’iyyar “the African Democratic Congress

Yan takarar shugaban kasa, a zaben ranar 16 ga watan Jeneru na shekara ta 2027 wato Alhaji Atiku Abubakar na Jam’iyyar “the African Democratic Congress (ADC), da Peter Obi na jam’iyyar “Nigeria Democratic Congress (NDC), dana “Allied Peoples Movement (APM), Seyi Makinde, da ” Peoples Redemption Party (PRP), Donald Dukea da kuma dan takaran shugaban kasa na jam’iyyar “the Social Democratic Party (SDP), Adewole Adebayo, zasu gudanar da taro a Abuja a ranar Litinin mai zuwa.

Jaridar Daily Truth ta Najeriya ta bayyana cewa Agendar taron shi ne, samar da kawance wanda zai sa dukkan jam’iyyun adawa su tsaya bayan dan takara guda don kada shugaba tinubu a zaben na shekara mai zuwa.

Labarin ya bayyana cewa da alamun shugaba tinubu yana iya kokarinsa na ganin ya sake dawowa kan kujerar shugabancin kasar a shekara mai zuwa.

Taron na ranar litinin dai da alamun shi ne taro mafi muhimmancin da za’a gudanar saboda zaben na shekara mai zuwa. Kuma mai yuwa ya samar da sauyi mai yawa a yanda sakamakon zaben zai kasance.

Wakilin Daily Trust ya bayyana cewa da farko dai ba’a dauki taron da muhimmanci a lokacinda aka gabatar da shawarar hakan a cikin yan makonni ko kwanakin da suka gabata ba. Amma a lokacinda taron ya kusa mutane da dama sun fahinci cewa taron yana da matukar muhimmanci kuma mai yuwa yayi tasiri a sakamakon zaben na shekara mai zuwa.

A aben shekara ta 2015 dai an yi irin wannan kawancen wanda ya hana shugaban kasa Goodluck Jonathan samun nasara a zaben shugaban kasa karkashin Jam’iyyar PDP na lokacin. Wanda kuma ya sanya Muhammadu Buhari zabebben shugaban kasa a karon farko.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted