Lebanon: Makaman Hizbulla Sun Fada Kan Cibiyar Bada Umurni Na Sojojin HKI A Arewacin Kasar Falasdinu Da Aka Mamaye

Kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon ta bada sanarwan kai hare hare kan sansanin sojojin HKI a kan tuddan Golan na kasar Siriya da aka mamaye.

Kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon ta bada sanarwan kai hare hare kan sansanin sojojin HKI a kan tuddan Golan na kasar Siriya da aka mamaye.

Tashar talabijin ta Almayadeen ta kasar Lebanon ta nakalto majiyar kungiyar na fadar haka a jiya Talata. Ta kuma kara da cewa ta yi amfani da makamai masu linzami 10 don wargaza cibiyar bada umurni da kuma sansanin sojojin HKI na –ar’ar. Labarin ya kara da cewa dakarun kungiyar sun sami nasarar kakkabo balom balom na leken asiri na HKI a sansanin na Ar’ar.

Tun ranar 8 ga watan Octoban day a gabata ne kungiyar ta shiga yaki da HKI musamman a yankunan arewacin kasar da ta mamaye don tallafawa Falasdinawa wadanda sojojin haramtacciyar kasar suke kashewa dare da rana.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments