Harkar Kiwon Lafiya Tana Daf Da Rugujewa A Yankin Zirin Gaza Sakamakon Killace yankin

Ana ci gaba da gargadin rugujewar tsarin kiwon lafiya a yankin Zirin Gaza Ma’aikatar Lafiya ta Falasdinu a Gaza ta sake fitar da sabon gargadin

Ana ci gaba da gargadin rugujewar tsarin kiwon lafiya a yankin Zirin Gaza

Ma’aikatar Lafiya ta Falasdinu a Gaza ta sake fitar da sabon gargadin rugujewar tsarin kiwon lafiya a yankin Zirin Gaza, bisa la’akari da yadda sojojin mamayar gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ke ci gaba da rufe kan iyakokin yankin Gaza don hana shigar da kayayyakin kiwon lafiya da na agajin jin kai na bil’Adama da kuma makamashi musamman man fetur.

Ma’aikatar lafiya ta Falasdinu a Gaza ta jaddada cewa: ‘Yan sa’o’i kadan ne suka rage harkokin tsarin kiwon lafiya su ruguje warwas a Zirin Gaza, sakamakon yadda aka gaza kawo man fetur da ake bukata don sarrafa injinan wutar lantarki a yankin saboda amfani a cikin asibitoci, motocin daukar marasa lafiya da jigilar ma’aikatan kula da kiwon lafiyan.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments