Gaza: An Kashe Jami’an Jinya Akalla 500 A Gaza Tun Lokacinda HKI Ta Fara Yaki A Gaza

Ma’aikatar lafiya ta zirin Gaza ta bada rahoton cewa sojojin HKI sun kashe jami’an jinya kimani 500 tun bayana fara yaki a ranar 7 ga

Ma’aikatar lafiya ta zirin Gaza ta bada rahoton cewa sojojin HKI sun kashe jami’an jinya kimani 500 tun bayana fara yaki a ranar 7 ga watan Octoban shekarar da ta gabata.

Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto majiyar ma’aikatar lafiya ta Gaza tana fadar haka a jiya Lahadi ta kuma kara da cewa jami’an jinyan da aka kashen sun hada da likitocin masu kula da marasa lafiya da kuma sauran kananan ma’aikatan kiwon lafiya.

Rahoton ya kara da cewa sojojin HKI daga cikin watan octoban da ya gabata  sun kashe Nas-nas, wato masu kula da marasa lafiya har 138, sannan sun kai hare hare kan asbitoci da cibiyoyin kiwon lafiya har 400 inda suka kashe likitoci, ma’aikatan jinya har da marasa lafiya.

Har’ila yau sun rusa asbitoci a kan wadanda suke cikisu,  daga ciki har da yan gudun hijira wadanda suke samun mafaka a asbitocin.

Daga karshe ma’aikatar ta bukata kasashen duniya su dauki matakan da suka dace na kare jami’an kiwon lafiya a zirin gaza daga hare haren sojojin HKI.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments