Isra’ila Ta Shiga Damuwa Kan Karancin Makaman Amurka

Karancin makamai masu linzami na Amurka yana damun gwamnatin Haramtacciyar kasar Isra’ila Wani mai sharhi kan harkokin sojan Haramtacciyar Kasar Isra’ila ya ce: Rashin na’urorin

Karancin makamai masu linzami na Amurka yana damun gwamnatin Haramtacciyar kasar Isra’ila

Wani mai sharhi kan harkokin sojan Haramtacciyar Kasar Isra’ila ya ce: Rashin na’urorin kakkabo makamai masu linzami da makamai masu linzami na Amurka shi ma yana daga cikin matsalolin da suke damun gwamnatin Amurka da burinta na son shimfida munanan manufofinta kan kasashe.

A rahoton da Kamfanin Dillancin Labaran Tasnim News Agency ta nakalto ta bayyana cewa: Yossi Yehoshua, wani mai sharhi kan harkokin soja na gidan talabijin na tasha ta 15 na Isra’ila, ya ce: “Rahotanni na Amurka sun nuna rashin isassun na’urorin kakkabo makamai masu linzami da makamai masu linzami; batun da ya shafi karfin sojojin gwamnatin Haramtacciyar kasar Isra’ila da ‘yancin daukar mataki a kan Iran kai tsaye.”

A halin yanzu, hukumomin tsaron gwamnatin Haramtacciyar Kasar Isra’ila sun yi gargadin a cikin ‘yan makonnin nan game da karancin kudaden da ake bukata don karfafa karfin soja da tsaro, amma ba kamar jami’an Amurka ba, har yanzu ba su bayar da cikakkun bayanai game da yanayin wadannan karancin kayayyakin yaki ko kuma sassan da abin ya shafa ba.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted