A wata sanarwar ta IRGC, sun sanar da kakkabo makamin Amurka mai linzami samfurin “Cruise” da safiyar yau Lahadi a garin Khurram-Abad dake yammacin Iran.
Sanarwar ta kuma ce; na’urorin kakkabo makamai na Iran sun harbo makami mai linzami samfurin “Cruise” da safiyar yau Lahadi.
Haka nan kuma dakarun IRGC sun ce, sun mayar da martani akan wuce gona da irin Amurka acikin kasar Iran a daren jiya da kuma siyar yau Lahadi a cikin matakai uku.
A matakin farko, Iran din ta kai hari akan cibiyar bayar da umarni ta sojan Amurka da kuma wuraren ajiyar jiragen leken asiri samfurin Mq9 dake sansanin soja na ” Yarima Hassan” a kasar Jordan.
Sai kuma hari a mataki na biyu wanda dakarun IRGC su ka kai wa jirgin ruwa na biyu da ya yi kokarin yin kutse a mashigar ruwan Hurmuz, da kuma kai wani harin akan sansanin sojan Amurka na “al-udaid” na kasar Qatar.
Mataki na uku na mayar da martanin kuwa ya fara ne da kai wa jiragen saman a jigilar makamashin da jragen yaki suke amfani da su wanda yake a kasar Oman.
A kasar Kuwaiti kuwa Iran ta kai hare-hare ne akan manyan makaman Patriot” da dakunan adana albarusai na sojan Amurka da yake a kasar Kuwait.Haka nan kuma da akwai jiragen sama marasa matuki na Amurka a cikin wannan sansanin.
A kasar Bahrain, Iran ta kai hari ne akan sansanin sojan Amurka, musamman wuraren ajiya jirage marasa matuki da na’urorin sadarwa.