Iran Ta Sanar Da Kwamitin Tsaro Na Mdd Keta Yarjejeniyar Dakatar Da Bude wuta Da Amurka Tayi

A hukumance kasar iran ta sanar da kwamitin tsaro na majalisar dinkin duniya game da keta yarjejeniyar dakatar da bude wuta da Amurka tayi inda

A hukumance kasar iran ta sanar da kwamitin tsaro na majalisar dinkin duniya game da keta yarjejeniyar dakatar da bude wuta da Amurka tayi inda ta fadada hare-haren ta a kasar iran, don haka ta yi kira ga kwamitin da ya dauki matakin gaggawa na dakatar da wannan zalunci  kuma ta gargadi Washington da ta shira karbar sakamakon mafi muni akan abin da ta aikata

a cikin wata wasika da jakadan din din din na kasar iran a majalisar dinkin duniya Amir Said Iravani  ya aikewa sakatare janar din majalisar ya nuna rashin amincewa  da keta yarjejeniyar dakatar da bude wuta da Amurka ta yi  inda ta kaddamar da sabbin hare-haren kan kasar iran wanda ya sabama dokokin majalisar da ma kasa da kasa

Ya aike da wannan wasikar ne bayan harin da Amurka ta kai a kudancin kasar iran da ya jawo mummunan asara da shahadar mutum guda daga cikin ma’aikata yan kwana kwana, kuma bayan nan jiragen yakin ta suka kai hari kan gadoji a kudancin kasar.

Rahotanni da suka fito sun nuna cewa Amurka ta kai harin ne a garin chabahar dake kudancin kasar inda suka hari Asibiti da kayayyakin  da suka shafi wutar lantarki , kuma sun hari garin Iranshahr da bushahar da ma wasu garuruwan.

daga karshe jadan na iran yayi kira ga kwamitin tsaro na majalisar da ya yi aiki da nauyin da ya rataya a wuyansa na daukar mataken gaggawa don dakatar da ci gaba da wannan zalunci, da kuma daukar matakin doka kan Amurka.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted