Rahotanni da suke fitowa daga birnin Damascuss na kasar Syria sun ambaci cewa; Wasu bama-bamai guda biyu sun tashi a kusa da ginin ma’aikatar yawon bude ido kuma kusa da masaukin shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron da yake ziyarar aiki a Syria.
Jim kadan bayan fashewar bama-bamai jami’an tsaro sun killace yankin da abin ya faru da dukkanin hanyoyin da suke kusa da yankin.
A can fadar mulkin Faransa “Élysée” an sanar da cewa ko kadan shugaba Emmanuel Macron bai ma ji karar fashewar bama-baman ba, kuma babu abinda ya sauya a tsarin ziyarar tashi.
Kamfanin dillancin labarun “Reuters” ya ambato majiyar tsaro ta kasar Syria tana cewa; Wasu abubuwa masu fashewa ne aka dasa a kusa da Hotel din da shugaba Emmanuel Macron sauka a cikinsa.
A yau Talata ne dai shugaban kasar ta Faransa ya fara ziyarar aiki a kasar ta Syria.
Ya zuwa yanzu dai an tabbatar da mutuwar mutane 4 da kuma jikkatar wasu 18.
Majiyar ‘yan sandan kasar ta Syria ta ce a tsakanin wadanda su ka jikkata da akwai ‘yan sanda 4.
Ma’aikatar cikin gida ta bayyana cewa; bama-baman sun fashe ne bayan da jami’an tsaron su ka gano su, suke kuma kokarin lalata su.