Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran: Mutunci, Kishin kasa Su Ne Manyan Abin Gado Da Jagora Ya Bari

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar iran Esma’ila Baqa’I ya fadi cewa manyan ababen gado da jagoran juyin musulunci na iran shahid Ayatullah Khamina’I ya bar

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar iran Esma’ila Baqa’I ya fadi cewa manyan ababen gado da jagoran juyin musulunci na iran shahid Ayatullah Khamina’I ya bar wa Alummar iran  shi ne mutunci, kishin kasam tsayin daka da kuma nuna juriya da jajircewa.

A cikin wani sako da ya aike da shi ta shafinsa na X da yake ishara game da gagarumin taron da aka yi a jana’izar jagoran jiyun musulunci na iran a nan birnin Tehran yace taro ne da ke nuna cewa an bude wani sabon shafi mafi muhimmanci a tarihi,

Miliyoyin iraniyawa sun yi bankwana da babban jagora a babban birnin kasar, wanda ba’a taba ganin irinsa ba a wannan zamanin, yace kyawawan halayensa za su ci gaba da wanzuwa har zuwa karnoni masu zuwa fiye da sunansa da kuma wannan zamani.

A ranar Alhamis ne za’a bizne jagora Ayatullah Khamina’I a hubbaren limami na 8 daga cikin limamai 12 na iyalan gidan manzon Allah tsira da aminci su tabbata garishi da alayensa a birnin mashhada bayan kwashe kwanaki biyu ana jana’izarsa a birnin qum da kuma kasar iraki.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted