Ma’aikatar Lafiya Ta Lebanon Ta Sanar Da Cewa: Mutane 19 Ne Suka Yi Shahada Cikin Sa’o’i 12

Ma’aikatar Lafiya ta kasar Lebanon ta sanar da cewa: Mutane 19 ne suka yi shahada a cikin awanni 24 da suka gabata, wanda ya kawo

Ma’aikatar Lafiya ta kasar Lebanon ta sanar da cewa: Mutane 19 ne suka yi shahada a cikin awanni 24 da suka gabata, wanda ya kawo jimillar wadanda suka rasa rayukansu zuwa 4,297

Ma’aikatar Lafiya ta Kasar Lebanon ta sanar da wani sabon karuwar adadin wadanda suka yi shahada sakamakon hare-haren wuce gona da irin sojojin gwamnatin Yahudawan Sahayoniyya kan kasar Lebanon, wanda ya tabbatar da cewa adadin wadanda suka yi shahada ya kai 4,297, yayin da adadin wadanda suka jikkata ya karu zuwa 12,196 tun bayan fara kai hare-haren zalunci kan kasar, bayan ta rubuta shahadan mutane 19 a cikin awanni 24 da suka gabata.

A cikin rahotonta na yau da kullun, Ma’aikatar Lafiya ta Lebanon ta bayyana cewa ta samu tabbacin shahadan mutane 19 a cikin awanni 24 da suka gabata, wanda hakan ya kara adadin wadanda suka rasa rayukansu sakamakon hare-haren wuce gona da irin Haramtacciyar kasar Isra’ila kan kasar tun daga ranar 2 ga Maris yawan shahidan sunkai zuwa 4,297 da kuma wadanda suka jikkata 12,196.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted