Shan Kayen Masu Takama Da Iko Da Girman Kai Na Duniya

A yau muna son yin magana game da yaƙin da ake tsammanin manyan masu takama da iko a duniya zasu yi nasara, amma sai akasin

Share

Hoton ya nuna yanayin yaƙi mai tsanani, tare da sojoji, fashe-fashe, makamai masu linzami, da kuma wata alama ta rikici tsakanin ƙasashe biyu a cikin yanayi mai cike da tashin hankali.

1

A yau muna son yin magana game da yaƙin da ake tsammanin manyan masu takama da iko a duniya zasu yi nasara, amma sai akasin hakan ya faru.

2

Duniya ba ta yi tsammanin cewa wata kasa za ta iya tsayawa a gaban manyan masu zalunci na duniya ba, har ma ta rikita lissafinsu da zai kai su ga shan kaye.

3

Wadannan ba kalmomi na ba ne.

4

John Mearsheimer, wani fitaccen masanin kimiyyar siyasa na Amurka ne ya yi ikirari da hakan a cikin wasu kalamansa na tarihi: Yaki da Iran bala’i ne ga Amurka.

5

Bari mu yi dubi zuwa ga wasu muhimman abubuwa 3 daga cikin abin da wannan hange nesa na wannan masani ya kunsaa: Na farko mafi muhimmanci shi ne yin lahani ga tasirin Amurka a duniya.

6

Mearsheimer ya ce bayan wannan yaƙin, babu wata ƙasa da za ta shiga ƙarƙashin lemar tsaro ta Amurka. Kasashen larabawan yankin Tekun Fasha dai sun gani da idanunsu cewa Amurka ba za ta iya kare kare su ba.

7

Iran ta tabbatar da cewa ita ce babbar kasa a yankin, kuma ta tabbatar da hakan a mashigar Hormuz. Me wannan ke nufi? Wannan yana nufin duk wani man fetur na yankin Tekun Farisa da za a fitar dole ne sai ya ratsa ta cikin Iran.

8

Amurka ba ita ce mai yanke shawara ba; Iran ita ce mai yanke shawara.

9

Na biyu; Babban shan kayen kungiyoyin masu mara baya ga yahudawan sahyuniya.

10

A cewarsa, yakin Trump a kan Iran domin faranta wa Netanyahu rai ne kawai. Amma me ya faru? Iran ta yi wa maharan mummunan lahani, inda za a iya ganin tasirin hakan hatta a kan titunan Amurka, su ma Isra’ilawa suna ganin hakan.

11

Har ma Amurkawa suna kokawa da cewa: Kun haifar ma kasarmu da matsaloli domin kawai ku kare manufofin Isra’ila.

12

Wannan yana nufin cewa tasirin masu fafutukar kare Yahudawan Sihiyona tsawon shekaru 70 ya fara rushewa.

13

Na uku; Amurka ta zama saniyar ware, yayin da sunan Iran ya shahara.

14

Dangantakar Amurka da Turai ta yi muni fiye da kowane lokaci, kuma sauran kawayenta na Asiya sun fara juya mata baya.

15

Amma Iran fa? Ta tabbatar da cewa ita kasa ce mai zaman kanta wadda ba ta buƙatar NATO ko kasancewa karkashin lemar Amurka. Ƙasa ce da za ta iya jure yaƙi. Kowa yana ganin yadda al’ummomin duniya suke aikewa da saƙonnin nuna cikakken goyon baya da fatan nasara ga Iran.

18

A takaice dai mahangar wannan farfesa Ba’amurke ita ce cewa Amurka ta sha kashi a yakin, kuma Iran ta kafa tarihi.

19

Iran ta tabbatar da cewa karfin iko na gaskiya shi ne yin tsayin daga da sadaukarwa da kuma kin mika wuya wajen kare hakkokinta, ta kuma tabbatar da cewa a Tehran ne ake yanke komai kan makomar kasar, ba a Washington ba.