YAKI DA NASARA

1 Idan Manufar ita ce canza gwamnati a Iran, me yasa yanzu ake maganar tattaunawa kan batun dage takunkumi da kuma amincewa da ci gaba

Share

Nasara tana bayyana ne ta hanyar dagewa kan manufa.

1

Idan Manufar ita ce canza gwamnati a Iran, me yasa yanzu ake maganar tattaunawa kan batun dage takunkumi da kuma amincewa da ci gaba da tace uranium? Bari mu yi dubi kan hakan domin gano manufar da kuma sakamako.

2

Daga farkon yakin, za a iya fahimtar manufofi daban-daban daga Amurka da Isra’ila, wadanda suke son cimmawa a yakin.

3

Na farko sauya komai a cikin Iran.

4

Wannan a cikin ilimin siyasa yana nufin matsin lamba domin canza tsari ko kuma gwamnati baki daya.

5

Na biyu, rusa shirin makamashin nukiliya baki daya, raunana gungun kwawancen ‘yan gwagwarmaya a yankin baki daya. Amma a madadin haka mene ne Iran ta gabatar daga nata bangaren?

6

Sharudda ne wadanda suke nufin kawo karshen yakin baki daya:
Kada a sake shiga wani yaki a nan gaba
Amincewa da ikon Iran a kan mashigar Hormuz
Amincewa da shirin Iran na tace uranium
Dauke dukkanin takunkumai na baya da na yanzu
Kawo karshen dukkanin kudurori na kwamitin tsaro, da kuma na kwamitin alkalan hukumar makamashin nukiliya ta duniya
Biyan diyya ga Iran
Ficewar dukkanin sojojin Amurka mayaka daga yankin
Daga da yaki a dukkanin fagage, da hakan ya hada da Lebanon

7

A duba dukkanin wadannan abubuwa, shin wani tsari na siyasa na Iran ya canza? Shin Iran ta janye daga matsayinta kan shirin nukiliya? Ko kuwa tasirinta ya kawo karshe a yankin? Ko kuwa ta canza matsayinta na neman ficewar sojojin Amurka daga yankin? A nan akwai abin da ya kamata mu yi la’akari das hi:

8

Lokacin manufa ta farko ita ce kawo karshen gwamnati, sai kuma aka kare kan yadda za a cimma matsaya kan a kan wasu batuwa, wannan na nufin an tashin daga manufar yakin ta farko.

9

Wannan shi ne hakikanin abin da ake nufi da hakikanin nasara.

10

Mai yiwuwa kowane bangaren zai iya bayyana lamarin daidai da mahangarsa.

11

Amma daga karshe wannan ke fayyace wane ne ya yi nasara ta hanyar dagewa kan bakansa, wane ne kuma ya ja da baya daga manufarsa ta farko.