1
Wane Lamuni Yarjejeniyar NPT Take Da Shi Ga Iran? Yarejejeniya ce wadda ya kamata ta kawo tsaro, amma ba ta kare barazana ko takunkumi ko kai hari ba.
2
Iran mamba ce wadda ta bayar da hadin kai amma mene ne sakamako? Matsin lamba mai tsanani, da kirkiro mata matsaloli, babu wani canji da ta gani.
3
Tambaya mai matukar muhimmanci: Shin lokacin da Amurka take yin watsi da irin wadannan yarjeniyoyi na kasa da kasa tana yin gaban kanta, shin a kan wane ne yin aiki da su ya zama wajibi?
4
Idan doka ta zama domin takura ku, ba domin kare ku ba, idan yarjejeniya ta zama domin matsin lamba a kanku ba domin amfaninku ba, shin ya yi daidai da hankali ku ci gaba da zama a cikinta?
5
Wasu na cewa ficewar na tattare da babban kalubale, haka ne, to amma kuma ci gaba da kasancewa a cikin abin da ba shi da amfani shi ma yana da nasa kalubale, daya daga ciki shi ne matsin lamba a kanku.
6
Mai yiwuwa lokaci ya yi da ya kamata mu yi tambaya a kan cewa: Mene ne amfanin wanzuwar Iran a cikin yarjejeniyar NPT?
7
Idan babu wata amsa takamaimai, Shin a hankalce ya kamata ta ci gaba da kasancewa a cikin wannan yarjejeniya?