Yiwuwar Bazuwar Yaki

Bari mu dan yi dubi a kan wannan taswira, da dama daga cikin masu sharhi suna cewa, mai yiwuwa yakin Amurka da Isra’ila a kan

Share

(Tak-Tak) (Tik-Tik) Yadda mai gabatarwa yake kwankwasa gilashin kamara kenan. yana cewa shin yakin nan zai iya bazuwa zuwa kofar gidan wasu kasashe?

(Tak-Tak) (Tik-Tik) Yadda mai gabatarwa yake kwankwasa gilashin kamara kenan.yana cewa shin yakin nan zai iya bazuwa zuwa kofar gidan wasu kasashe?
2
Bari mu dan yi dubi a kan wannan taswira, da dama daga cikin masu sharhi suna cewa, mai yiwuwa yakin Amurka da Isra’ila a kan Iran ya kara bazuwa zuwa wasu yankuna.
3
Ya zo a cikin wani rahoto cewa kasashen yankin tekun Fasha su ne a sahun gaba na wannan yaki.
4
Domin kuwa su ne suke daukar bakuncin manyan sansanonin sojin Amurka da suke kaiwa Iran hari.
5
Tabbas kuwa Lamarin zai yi mummunan tasiri a cikin sauri ga kasashen da suke daukar nauyin bakuncin sansanonin sojin Amurka.
6
Amma kuma wannan batu ba zai takaita da kasashen yankin Tekun Fasha ba kawai, wasu dalilan za su iya sanya tasirin hakan ya kara bazuwa zuwa wasu yankunan.
7
A Lebanon Isra’ila tana ci gaba da kai hare-hare, wanda zai iya yin tasiri ga makomar siyasa da tattalin arzikin kasar, haka nan a Iraki akwai sansanonin sojin Amurka, wanda zasu iya fuskantar hare-haren martani na soji.
8
Baya ga haka kuma tasirin wannan yaki a kan makomar kasuwar makamashi, musamman batun mashigar Hormuz.
9
Sannan kuma a duk lokacin da wasu kasashe suka shiga cikin yakin, hakan zai baiwa Iran damar kara fadada taswirar mayar da martani.
10
Wannan zai sanya Iran ta mayar da martani a duk inda Amurka da Isra’ila suka saka kafarsu.
11
Tasirin wannan yaki zai iya kaiwa har zuwa kan iyakokin kasashen turai.
12
Wannan yana zuwa a daidai lokacin wasu rahotanni ke cewa an bude manyan wuraren ajiyar danyen mai a kasashen Italia da Japan.
13
Masana kan harkokin tsaro suna cewa, harin da Amurka ta kaddamar a kan tsibirin Kharg na Iran, shi ma zai iya yin mummunan tasiri a kan harkar fitar da makamashi har da sauran harkokin kasuwanci a duniya.