Gaza: Watanni 4 Bayan Tsagaita Wuta Har Yanzu Babu Abinda Ya Sauyawa Mutanen Gaza

 Rahotannin da suke fitowa daga Gaza suna nuni da cewa, duk da gushewar watanni 4 daga tsagaita wutar yaki , rayuwar falasdinawa ta yau da

 Rahotannin da suke fitowa daga Gaza suna nuni da cewa, duk da gushewar watanni 4 daga tsagaita wutar yaki , rayuwar falasdinawa ta yau da kullum ba ta sauya ba.

Haka nan kuma rahotannin daga Gaza suna nuni da yadda  mutanen yankin ke ci gaba da fama da yunwa da kuma rashin ci gaba fuskantar hare-hare daga ‘yan sahayoniya.

A yankin ‘al-mawasi” dake Khan Yunus,iyalai da dama da su ka yo hijira daga Rafah da wasu wurare suna rayuwa a cikin fargaba da tsoro saboda babu abinda ya sauya musu tun bayan tsagaita wutar yaki da aka shelanta.

Wata ‘yar hijira a yankin ta fada wa tashar talabijin din ‘aljazira’ cewa, ko sau daya harsashin da ‘yan mamaya suke harbawa bai taba tsayawa ba dare da rana, haka nan kuma kullum suna jin motsin tankokin yaki.

Har ila yau ta bayyana cewa, ba ta samun wadataccen abincin da za ta bai wa ‘danta wanda yake fama da rashin lafiya.

Daga lokacin da aka tsagaita wutar yaki a Gaza, babu wata rana da ‘yan mamayar ba su kai hari da yake haddasa yin shahadar Falasdinawa da dama. Majiyar Falasdinawa ta ce,adadin wadanda su ka yi shahada a wannan tsakanin sun haura 500, wani adadin mai yawa kuma ya jikkata.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted