Kasashe 85 sun yi tir da Isra’ila kan shirin gina matsugunai a Yammacin Kogin Jordan

Kasashe 85 na Majalisar Dinkin Duniya sun yi Allah wadai da matakin da Isra’ila ta dauka a baya bayab nan na daukar sabbin matakai da

Kasashe 85 na Majalisar Dinkin Duniya sun yi Allah wadai da matakin da Isra’ila ta dauka a baya bayab nan na daukar sabbin matakai da nufin “fadada kasancewarta ba bisa ka’ida ba” a Yammacin Kogin Jordan da aka mamaye.

Kasashen sun yi Allah wadai da shawarar a cikin wata sanarwa ta hadin gwiwa, suna fargabar cewa matakin zai kai ga mamaye yankin Falasdinawa.”

“Muna Allah wadai da shawarar Isra’ila da matakan da ta dauka na fadada kasancewarta ba bisa ka’ida ba a Yammacin Kogin Jordan.

Wadannan shawarwarin sun saba wa wajibcin Isra’ila a karkashin dokokin kasa da kasa kuma dole ne a sauya su nan take,” in ji kasashen 85 na Majalisar Dinkin Duniya, ciki har da Saudiyya, China, Faransa, Pakistan, da kuma Rasha.

Wadannan kasashe sun sake nanata kin amincewarsu da duk matakan da aka dauka na sauya tsarin al’umma, yanayi, da matsayin yankin Falasdinawa da aka mamaye tun 1967, ciki har da Gabashin Kudus.

Sanarwar ta yi gargadin cewa irin wadannan matakan sun saba wa dokokin kasa da kasa kuma suna kawo cikas ga kokarin da ake yi na samar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted