Geneva: A Yau Talata Za A Fara Tattaunawa Tsakanin Iran Da Amurka A Birnin Geneva

Kamfanin dillancin labarun “Irna” ya nakalto wata majiya ta kusa tana cewa; Da tsakiyar ranar yau ne za a bude tattaunawar  Nukiliya a tsakanin tawagogin

Kamfanin dillancin labarun “Irna” ya nakalto wata majiya ta kusa tana cewa; Da tsakiyar ranar yau ne za a bude tattaunawar  Nukiliya a tsakanin tawagogin Iran da na Amurka a birnin Geneva na kasar Switzerland ta hanyar shiga tsakanin kasar Oman.

Tattaunawar ta yau ita ce zango na biyu a tsakanin bangarorin biyu, bayan wacce aka bude a kasar Oman.

Iran ta bayyana cewa, batun shirinta na Nukiliya ne kadai za a yi Magana akansa, da za ta bukaci a dauke mata takunkumai domin ta daga kafa akan Shirin nata.

Wakilin kamfanin dillancin labarun “Irna” zuwa kasar ta Swissland ya ce; Daukewa Iran takunkumai, da kuma kare manufofin kasa, su ne muhimman jigon da Iran za ta bijiro da su, a yayin tattaunawar Nukiliya da Amurkan.

A jiya Litinin da Safe ministan harkokin wajen jamhuriyar Musulunci ta Iran Abbas Arakci, ya gana da shugaban hukumar makamashin Nukiliyar Iran ta kasa da kasa Refael Gorssy a birnin Geneva. Bangarorin biyu dai sun yi musayar ra’ayi akan tattaunawa da Amurka.

 Haka nan kuma ministan harkokin wajen na Iran ya yi wata ganawar da takwaransa na kasar Oman inda su ka tattaunawa batun tattaunawar da kuma mahangar Iran akan dauke mata takunkumai.

A yayin wannan ganawar, ministan harkokin wajen na Iran ya yaba wa kasar Oman saboda rawar da take takawa a shiga tsakani da Amurka.

A nashi gefen, ministan harkokin wajen kasar Oman, “Badr Bu sa’idi” ya yi Ishara da tsohuwar da take a tsakanin kasashen Iran da kasarsa, da kuma rawar da Iran din take takawa wajen tabbatar da zaman lafiya a cikin wannan yankin na yammacin Asiya.

Haka nan kuma ya yi fatan ganin cewa za a cimma matsaya  a wannan tattaunawar ta hanyar amfani da diplomasiyya.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted