Iran: Za’a Gudanar Da Addu’o’ii Saboda Cika Kwanaki 40 Da Shahadar Shahidan Fitinar Amurka Da HKI

Majalisar shiryawa da kuma yada al-adun musulunci a nan Iran yayi kira ga jami’a su halarci zaman addu’a da karatun Al-kur’ani ga shahidan ranakun 8

Majalisar shiryawa da kuma yada al-adun musulunci a nan Iran yayi kira ga jami’a su halarci zaman addu’a da karatun Al-kur’ani ga shahidan ranakun 8 da 9 ga watan Jenerun wannan shekarar, wadanda yan ta’adda wadanda suke samun goyon bayan kasashen yamma suka kashe.

Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Majalisar tana fadar haka a farkon wannan makon kuma ta kara da cewa tarurrukan za’a gudanar da su a duka fadin kasar ne, amma a nan birnin Tehran za’a gudanar da taron 40 na shahadan fitina ne a Musallah na Imam Khomaini (q) dake nan tsakiyar birnin Tehran a yau Talata.

Labarin ya kara da cewa manufar adu’o’in shi ne neman Allah ta’ala ya karbi shahadar wadan nan bayin sa, ya kuma bawa iyalansu hakurin jurewa shahadar masoyansu. Banda haka labarin ya kara da cewa wadan nan shahidai sun taka rawar a zo a gani wajen dushe wutar fitina wadanda wadanda kasashen yamma da HKI suka kunna a kasar don sharer fagen kifar da gwamnatin JMI.

A ranar 11 ga watan Jeneru na wannan shekara ne mutanen kasar Iran suka fito kwansu da kwarkwatansu suka kashe wutar fitina wacce mayakan kundiyar ISIS masu samun goyon bayan kasashen yamma suka kunna a ranar 8 da 9 ga watan.

Gwamnatin JMI ta bada sanarwan cewa an kashe jami’an tsaro da kuma mutanen gari kimanin 2,427 a wannan fitinar. Sannan an kashe jimillar mutane 3,117 idan an hada da yan ta’addan da kuma masu taimaka masu daga cikin gida.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted